Sai da NIN ayi REGISTAR FACEBOOK Inji Prince Abdul Tilde

 Ana wata ga wata! 

Wani Matashi Mai Suna Prince Abdul Tilde Dan asalin garin Tilde Dake karamar Hukumar Toro Jahar Bauchi Ya aikewa Ministan Sadarwa Da Wasika Akan Abinda akeyi a Facebook

BUDADDIYAR WASIKA ZUWAGA DR MALAM ISA ALI PANTAMI MINISTAN SADARWA AKAN SOCIAL MEDIA


Assalamualaikum Malam dafatan kananan Lafiya Allah yasa haka amiin.

Malam munsan kana iya bakin kokarinka a matsayinka na Ministan Sadarwa Kuma duniya ta tabbatar da kokarinka sannan da jajircewarka akan aikin Daya shafi Communication Muna Godiya da wannan. 

Malam Harga Allah yanzu akwai abinda yafi Kiran waya saurin tada zaune tsaya shine Social Media Kuma a Social Media dinma bakamar Facebook.

Bansan Facebook nawa take biyanku shares ba amma koma dai nawane Yakama kaduba lamarin Facebook dinnan domin kawo sabon salon yin Rigistan Facebook idan da Halima ace kowa saiya hada Katin Dan kasa wato NIN kafin yasamu daman yin Facebook a Nigeria.

Idan akace kowa sai yanada NIN zaiyi Facebook kaga kowa za'asan asalinsa da Kuma inda yafito to anan za'a samu Labaran gaskiya daga bakin Jama'a sannan kowa yayi badaidai ba direct ansan inda yake sabanin yanzu yadda kowa yake bude Facebook Account da sunan dayaga dama Kuma ya hidin identity dinsa.

Malam nasan wannan bawani Abu bane dazai gagareka Dan Allah malam Aduba Harkar Social Media Sosai ayi gyara.

Dan Allah kutayani Yada wannan Sako nawa harya isa izuwa wajen Malam Kuma Ministan Sadarwa NAGODE.


RUBUTAWA

Prince Abdul Tilde

25/05/2022

Post a Comment

0 Comments