Mal. Nasiru El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna ya fadawa Gwamnoni da mutanen kudancin Nijeriya gaskiya game da zaben 2023

Mal. Nasiru El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna ya fadawa Gwamnoni da mutanen kudancin Nijeriya gaskiya game da zaben 2023
Gwamnan jihar kaduna Malam Nasiru El Rufa,i ya fadawa gwamnonin kudancin Nijeriya cewa ba wanda zai tilasta ma al,ummar arewa mika mulki zuwa kudancin Nijeriya.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya faɗawa gwamnonin kudu cewa ba zasu tilastawa arewa ta mika musu mulki Nijeriya ba.

Domin A cewar El Rufa,i kundin tsarin mulkin Nijeriya bai tanaji mulkin karɓa-karɓa ba, kuma babu tsarin karba - karba a cikin dokokin jam'iyyar APC 

El Rufa,i yace a cikin jam,iyar PDP ne akwai wannan dokar amma su yan kudu da kansu suka karya ta lokacin mulkin marigayi Yar'adua


Jaridar DAILY TRUST ta rowaito cewa El-Rufa'i ya faɗi haka ne A yayin da yake tsokaci kan bukatar gwamnonin kudu na cewa yankinsu ne zai fitar da shugaban ƙasa wanda zai gaji Buhari a shekarar 2023.

Malam Nasiru El Rufa,i wanda ya bada shawarar baiwa Kudancin Nijeriya shugaban ƙasa, yace gwamnonin kudu sun ɗauki abun da zafi, da har zasu ce wajibi ne a ba su shugaban ƙasa a 2023.

Ba zaku tilasta mana sai mun baku shugaban ƙasa ba domin amfani da kalmar 'Ɗole' na nufin ko muna so ko bamu so, meyasa zaku kawo batun wajibi a harkokin siyasa?"

Babu dokar mulkin karba-karba a kundin tsarin mulki, waɗannan abubuwan ana yinsu ne domin haɗin kai da sulhu.

Kowace jam'iyyar siyasa tana da nata dokoki kuma babu wata doka a APC da ta amince a yi mulkin karba-karba a cikin Nijeriya. 

Bugu da ƙari gwamna El-Rufa'i yace jam'iyyar PDP da ke da tsarin mulkin kama-kama, "Sun karya dokar lokacin mulkin marigayi shugaba Umaru Musa Yar'adua da Goodluck Jonathan.

Saboda haka, wani ya fito yace kada ɗan Najeriya ya nemi shugaban ƙasa kawai saboda yankin da ya fito, babu makamancin haka a kundin tsarin mulkin Nijeriya da jam,iyar APC. 

Wato jama,a Ni Abubakar A Adam Babankyauta ina mai tabbatar muku da cewa magana ta gaskiya itace mulkin Nijeriya 2023 sai dan Arewa domin tunda muka dawa tsarin mulkin demokaradiyya 1999 yau shekara 22 kenan idan mukakai shekarar 2023 yazama shekara 24 kenan.


Gabaki daya shekara nawa dan Arewa yayi yana mulkin Nijeriya cikin shekaru 24.


1) Obasanjo daga 1999 zuwa 2007

Shekaru 8

2) Umaru musa`yar`adua daga 2007 zuwa 2009

Shekaru 2

3) Jonathan daga 2009 zuwa 2015

Shekaru 6 

4) Sai Buhari ya fara daga 2015 inda ake saran zai kai 2023 

Shekaru 8

Yanzu idan har Allah yasa buhari yayi shekara 8 akan mulkin Nijeriya zai zama cewa yan arewa sunyi shekara 10 kenan a yayin da su kuma yan kudancin Nijeriya sukayi shekara 14 akan mulkin Nijeriya. 

Yadda lissafin yake shine umaru musa `yar`adua yayi shekara 2 shi kuma buhari idan har yakai 2023 yayi shekara 8 kenan kunga 2+8=10 yanzu yan arewa sunyi shekaru 10 kenan suna mulkin Nijeriya daga 1999 zuwa 2023.

Su kuma yan kudancin Nijeriya Obasanjo yayi shekaru 8 Ayayin da shi kuma Jonathan yayi shekaru 6 kunga 8+6=14 yanzu yan kudancin Nijeriya sunyi shekaru 14 suna mulkin Nijeriya daga 1999 zuwa 2023

Acikin babun adalci shine idan har yan kudancin Nijeriya zasuma kansu adalci yanzu yazama dole subar dan arewa ya gaji buhari a shekarar 2023 domin samun daidaitan shugabanci a shekarar 2027. 

Muna rokon ubangiji Allah  ya bama kasar mu Nijeriya jagorori nagari.

Daga Abubakar A Adam Babankyauta.

Post a Comment

0 Comments