An bayyana jimillar kudin da kowane dan majalisar wakilai ke karba duk wata||

 An bayyana jimillar kudin da kowane dan majalisar wakilai ke karba duk wata

 


Hon Simon Karu ya fadawa mahalarta taron cewa kowane dan majalisa yana karbar miliyan 9.3 gaba daya a matsayin albashi da kudin gudanar da shi

 Adadin da Karu ya bayar an samu sabani ne daga wani dan majalisa, Ossai Nicholas Ossai. 

 Simon Karu, dan majalisar wakilai ya bayyana jimillar kudin da kowane dan majalisar ke karba duk wata.

 Dan majalisar wanda ke wakiltar mazabar tarayya ta Kaltungo / Shongom na jihar Gombe ya ce albashin dan majalisar a hukumance shi ne N800,000.

 Wannan shine babban alawus da muke karba kowane wata - memban NASS yayi cikakken bayani.

 Karu ya kuma bayyana cewa kowane memba kuma yana karbar N8.5 miliyan duk wata domin gudanar da ofis, hakan yasa ya zama miliyan 9.3.

 Aminiya ta ruwaito cewa ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, a Umaru Musa Yar’adua Centre, da ke Abuja, lokacin da yake magana a wani taron kan tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin mulki.


 Ya ce:

 Albashin ma’aikaci a hukumance, Majalisar Wakilai wanda ni kuma nake karba duk wata shi ne N800,000. “Na fada maka zan fada, me ya sa ba ka jira na fadi ba?  Kudin da ofishin yake kashewa na dan majalisar wakilai ya kai miliyan N8.5.  Ku da kuka sani, ku sani na fadi ainihin abin da yake. "Duk da haka, wani dan majalisar wakilai Ossai Nicholas Ossai ya gaya wa taron cewa su yi watsi da alkaluman da abokin aikinsu ya ambata. 

 Ossai ya ce bai taba samun irin wannan kudi ba tun lokacin da aka zabe shi a Majalisar Tarayya.

 A halin yanzu, majalisar wakilai ta janye kudirin dokar albarkatun ruwa wanda karamar majalisar ta zartar watanni biyu da suka gabata.

 Takardar dokar mai cike da cece-kuce a ranar Talata, 29 ga Satumba, ta haifar da rikici yayin zaman majalisar yayin da mambobin majalisar suka ki amincewa da tsarin da aka bi wajen zartar da kudirin.

 Hayaniya tsakanin 'yan majalisar ta fara ne lokacin da Benjamin Mzondu mai wakiltar jihar Benuwe ya gabatar da kudiri a karkashin Matter of Privilege.

Post a Comment

0 Comments